Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza

Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza

A yau Talata, wata kotu da ke zaune a garin Ile-Tuntun a Ibadan ta katse igiyar auren wasu ma'aurata da sukayi shekaru 11 suna tare amma a yanzu suka bukaci kotu ta raba auren saboda cin amana da mijin yace matar tana yi masa.

Bayan zartar da hukuncin kotun, auren da ke tsakanin Timisiyu Adegoke da uwargidarsa, Modupe, mai yara biyu ya kare. A yayin da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Cif Henry Agbaje tace ya zama dole ne ta raba auren saboda ma'auratan sun gaza sulhunta kansu.

Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza
Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza

Matar, Modupe tayi ikirarin cewa mijin nata baya nuna mata son da kauna kuma baya kulawa da ita da yaranta, galibi ma sai duka kawai yake nakada mata duk lokacin daya bushi iska.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

A bangarensa, Tirmisiyu ya musanta zargin inda ya misalata matar tasa da kwaririyar karuwa kuma makaryaciya. Ya kara da cewa, "Ranka ya dade, babban dalilin rikici na da Modupe shine cin amana na aure hakan yasa bazan iya amincewa da ita ba.

Tirmisiyu ya cigaba da cewa, sau da yawa yana kama ta lokacin da take kulla harka da wasu mazajen kuma ya kaita kara wajen wasu daga cikin yan uwansu, abokanai har ma da makwabta.

Sai dai yace ta dara shi wayyo sosai don galibi tana boye hujjar cin amanar nata cikin manyan wayoyinta guda biyu wanda take amfani dashi wajen kulla zumunta da masoyanta inda yayi ikirarin cewa akwai hotunan ta na tsiraici da take aikawa masoyan ta.

"Ranka ya dade, idan aka duba, akwai sakonin soyaya, hotunan batsa, da kuma hirar yadda suka lalata ta morewa idan sun hadu duk a cikin wayar nata. "Tayi tafiyarta, bana bukatar ta a matsayin mata ta har abada," inji shi.

Kamfanin dillanci labarai ya ruwaito cewa mijin ya gabatar da wayar android guda daya da kuma wata kirar Tecno 230 a matsayin sheda wanda ya kwace a hannun matansa don ya nuna wa kotu irin cin amanar da take yi masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel