Yadda masarautar Saudiyya keyi da 'yan Shi'a a yau

Yadda masarautar Saudiyya keyi da 'yan Shi'a a yau

- Yariman kasar Saudiyya, Bin Salman yace ba gaskiya bane farfagandar da wasu ke yadawa ne cewa ana musgunawa yan Shi'a a Saudiyya

- Yariman yace yan Shia suna zaman su lafiya a Saudiyya kuma suna ma rike da mukamai a cikin gwamnatin kasar ta Saudiyya

- Bin Salman yace matsalar da suke dashi kawai ya danganci yadda gwamnatin kasar Iran keyin katsalandan cikin harkokin gida na Saudiyya ne

Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Mohammad bin Salman yayi tsokaci kan yadda wasu kafafen yadda labarai na kasashen yamma ke yadda farfaganda na cewa kasar Saudiyya tana musgunawa 'yan Shia wanda kuma a zahirin gaskiya ba haka zancen yake ba.

Ya cigaba da cewa yan Shi'a suna da damar suyi taruruka, walima da kuma gabatar da wa'azi da kasidu bisa fahimtar akidarsu ba tare da kowa ya musguna musu ba abinda kawai basu da ikon yi shine gudanar shine zaman makoki na tunawa da rasuwar Imam Hussain (R.A) saboda dukkan mazhabobi 4 na addinin musulunci basu amince mutum ya doki kansu saboda mutuwar wani ba.

Yadda masarautar Saudiyya keyi da 'yan Shi'a a yau
Yadda masarautar Saudiyya keyi da 'yan Shi'a a yau

Hakazalika, gwamnatin Saudiyya kuma bata amince da yin tattaki a kan tittuna ba kamar yadda yan shi'an sukeyi a wasu kasashen. Hasali ma babu wanda dokar kasar Saudiyya ta amince ya aikata hakan ko da ahalul Sunna ne shi.

DUBA WANNAN: Idan ba'ayi taron gangamin ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

"Idan ka ziyarci masallacin Harami, zaka lura cewa akwai dimbin yan Shi'a da ahlul Sunna suna sallah tare. Wannan shine babban alamar cewa dukkan musulmi yan uwan juna ne kuma ba'a nuna banbanci tsakanin dukkan musulmin duniya.

Yariman na kasar Saudiyya yayi wannan maganganun ne a wata sabuwar hirar da yayi da babban Editan jaridar Atlantic, Jeffery Goldberg inda suka tattauna a kan kungiyoyin addinin musulunci da ke kasar Saudiyya.

Da Goldberg yayi wa Yariman tambaya a kan Wahabiyanci a kasar, ya amsa da cewa tabbas akwai Wahabiyanci a kasar, kuma ya kara da cewa hakan baya nuna cewa an ware 'yan Shia. Yace akwai yan Shia a cikin gwamnatin inda har ya bayar da misalin cewa dan Shia ne ke shugabancin babban jami'ar kasar Saudiyya.

Goldberg kuma ya sake tambayarsa ko rikicin da ke tsakanin Saudiyya da Iran yana da nasaba da addini. Bin Salman ya amsa da cewa, "Kamar yadda na fada a baya, yan Shi'a na zaune lafiya a Saudiyya. Bamu da matsala da yan Shi'a, rikicin mu da salon siyasar gwamnatin Iran ne. Bamu amince suna da ikon da zasu rika yi mana kutse cikin harkokin cikin gidan mu ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel