Yaki da yan bindiga: Yansanda sun kwato manyan bindigu guda 84 a jihar Kaduna

Yaki da yan bindiga: Yansanda sun kwato manyan bindigu guda 84 a jihar Kaduna

Rundunar Yansandan jihar Kaduna ta sanar da kwato muggan makamai guda 84 daga hannun mazauna jihar Kaduna, tare da alburusai 120, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Austin Iwar ya bayyana haka ga manema labaru a ranar juma’a 6 ga watan Afrilu, inda yace daga cikin bindigu akwai AK47 guda 20, bindigun toka 42, Bindigar ‘Pump Action’ guda 15, da kananan bindigu 7.

KU KARANTA: Tsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa

Bugu da kari Yansanda sun kwato Babura guda 3 kirar Boxers, kwalekwalen Sojoji guda 3, hulunan Sojoji 2, kwari da baka 2, gariyo guda 40, adduna 30 da layoyin tsafe tsafe, inji kwamishina Iwar.

Yaki da yan bindiga: Yansanda sun kwato manyan bindigu guda 84 a jihar Kaduna
Bindigu

Kwamishinan ya cigaba da fadin sun guadanar da wannan aikin kwato makamai ne bisa umarnin bababn sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris, a wani mataki na yaki da safarar makamai da shigo dasu kasa Najeriya. Kwamishinan ya kara da cewa suna aiki kafada da kafad da kwamitin kwace makamai na gwamnatin jihar Kaduna.

“Kwalliya ta biya kudin sabulu a aikin da muke yi tare da hadin gwiwar shuwagabannin al’umma, wanda hakan yayi sanadin da wasu miyagun mutane su 760 suka tuba daga aikata miyagun laifuka a karamar hukumar Anchau. Haka zalika mun kama yan Sara suka 70, inda guda 20 sun fuskanci shari’a.” Inji shi.

Daga karshe yayi kira ga jama’an jihar Kaduna da su zauna lafiya, tare da bin doka da ka’ida, sa’annan su kai karar duk wani mutumin da basu gane take takensa bag a hukumomin tsaro mafi kusa dasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel