Hotunan Sabbin Dakarun Sojin Sama 195 da aka yaye a garin Kaduna
A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar Sojin Sama ta Najeriya, ta yaye sabbin dakaru 195 daga makarantar horaswa ta NAF Military Centre dake garin Kaduna bayan tsawon watanni shidda da suke shafe na koyan makamar aikin.
Hukumar ta yaye kimanin dakaru 195 da suka hadar har da mata 16. Hukumar ta bayyana cewa, kimanin dakaru 198 suka shigi wannan makaranta ta horaswa wanda 3 daga ciki suka gaza sakamakon yanayi da wahalhalu na koyon aiki.
Ministan Tsaro na kasa Alhaji Mansur Dan Ali, shine ya jagoranci wannan biki na yaye dakarun tare da manyan dakarun soji da kuma jiga-jigan gwamnatin kasar nan da suka hadar har da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i.
Ministan ya gargadin sabbin dakarun da su nuna zakakuranci tare da bajinta ta gari wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare daura damara ta tunkarar kalubalan tsaro da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.
KARANTA KUMA: Fiye da ma'aikata 20,000 muka dauka cikin shekaru 3 domin don ƙarfafa dakarun Soji - Mansur Dan Ali
Alhaji Dan-Ali ya kuma yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadun Buhari da yake ci gaba da bayar da muhimmanci wajen karfafa hukumar Sojin kasar nan tare da inganta jin dadin su.
Ministan ya kuma sake yabawa shugaban hafsin sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Sadique Abubakar, dangane da jagoranci nagari da yayi ruwa da tsaki a nasarorin da hukumar Sojin ta ke ci gaba da samu.
A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar Sojin kasa ta cafke wasu barayin shanu hudu a jihar Bauchi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng