Tsohon Ministan Najeriya ya rubuta badakalar da aka tafka a kasar nan a baya

Tsohon Ministan Najeriya ya rubuta badakalar da aka tafka a kasar nan a baya

- Za a rubuta littafin tarihin wani tsohon Ministan Najeriya M.T Mbu

- Mbu yayi bayani game da mulkin Jonathan da ‘Yaradua kafin ya rasu

- Tsohon Ministan ya bayyana inda ‘Yaradua ya samu matsala a mulki

Mun samu labari cewa wani tsohon Ministan harkokon wajen Najeriya Marigayi MT Mbu wanda ya rasu a shekarar 2012 ya kawo labarin abubuwan da su ka faru a Najeriya a baya har zuwa lokacin Marigayi tsohon Shugaban kasa Umaru Musa ‘Yaradua.

MT Mbu a littafin da yake rubutawa mai suna ‘Dignity in service’ kafin ya rasu ya bayyana cewa Marigayi Umaru Musa ‘Yaradua da ma Mataimakin sa da ya gaje shi watau Goodluck Jonathan ba su shirya mulkin kasar nan ba ya fada kan su.

KU KARANTA: An bayyana adadin Sojojin da Buhari ya dauka aiki a mulkin sa

Tsohon Ministan kasar yace Goodluck Jonathan ya gaza yakar rashin gaskiya da sata ne saboda ya tsaya kokarin yi wa mutanen sa na Ijaw hidima. A cewar tsohon Ministan, Peter Odili ya kamata yayi mulki a 2007 amma wasu su ka hana don dole.

Iyalin Marigayin sun bayyana cewa kwanan nan za a kaddamar da wannan littafi da Mbu ya hada a dakin taro na Shehu ‘Yaradua a Abuja. Mbu yayi kaca-kaca da Gwamnan Kuros Riba a littafin ya kuma bayyana badakalar da aka tafka a Jamhuriya ta farko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel