Nigerian news All categories All tags
Mutanen mu Inyamurai za su zama Bayi a Najeriya idan aka yi sake - Rochas Okoracha

Mutanen mu Inyamurai za su zama Bayi a Najeriya idan aka yi sake - Rochas Okoracha

- Rochas ya fadi babban abin da ya sa ya ke yi wa Inyamuran Najeriya kuka

- Inyamurai ba su cika fitowa yin zabe ba kamar yadda ya kamata a Najeriya

- Alkaluma sun nuna haka wanda Gwamnan yace zai sa su zama Bayin kasar

Mun samu labari daga majiyoyi da dama a farkon makon nan inda Gwamnan Jihar Imo Rochas Owelle Okorocha ya bayyana abin da yake sa shi yi wa mutanen Kudancin Kasar nan kuka a duk rana ta Allah.

Mutanen mu Inyamurai za su zama Bayi a Najeriya idan aka yi sake - Rochas Okoracha

Gwamna Okorocha ya gargadi Inyamuran Najeriya

Gwamna Okorocha yace idan ya duba alkaluman masu zabe a Kasar nan kamar yadda Hukumar INEC ta saki ya ga yadda Inyamurai ba su fitowa zabe sai ya ji yana kuka. Gwamnan yace mutanen su za su zama Bayi a Kasar nan.

KU KARANTA: Ana shirin dawo da Oyegun ta bayan gida a APC

Rochas Okorocha yayi wannan jawabi ne a sakon sa na wannan makon na bikin Easter da Kiristoci su kayi. Gwamna Okorocha ya gargadi Mutanen Yankin na Kudu maso gabashin kasar da su fito ayi zabe da su ko kuma ayi ba su.

Gwannan na Jam'iyyar APC mai mulki ya nemi rikakkun Malaman addini su sa baki wajen ganin jama'a sun fito kwan-su da kwarwata wajen zabe. Yanzu haka dai Gwananan na shirin kakaba surukin sa ya gaje sa a matsayin Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel