Za'a Bude Gidajen Kallon Da Za Su Cakuda Samari Da Y'an Mata a Kasa Mai Tsarki
Kasar Saudiyya, zata aiwatar da wata yarjejeniyar gina katafaren gidajen kallo wato sinima guda 40 a birane 15 dake kasar cikin shekaru biyar masu zuwa.
Bayan shafe shekara 35, ma'aikatar Yada Labarai da Al'adu ta kasar ta Saudiyya, ta sami lasisin da ya baiwa kamfanonin fina-finai a ko'ina suke a duniya damar yin sinima a cikin kasar.
Kimanin gidajen kallon dari uku da hamsin 350 ake sa ran budewa, dauke da shafukan kallo dubu biyu da dari biyar 2,500, wanda zai baiwa mata da maza damar zama su sha kallo guri guda ba tare an raba jinsin maza da mata ba.
Saudiyya, na da adadin mutane milyan talatin da biyu 32,000,000 kuma mafi yawansu samari ne. Ana sa ran Saudiyya za ta zama gurin hada-hadar fina-finai da ta fi kowacce kasa a kasashen larabawa.
DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta gayyato DJ daga Turai domin kawai a rakashe
Ko a kwanakin baya, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar, a karo na farko a tarihinta, masarautar kasar Saudiyya ta gayyato fitaccen masanin kida (DJ) domin cashewa da kida.
Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Saudiyya da aka tabo gayyato makidin zamani domin kawai a sha kida a cashe da rawa.
Shafin Arabian Business dake yanar gizo ya wallafa cewar gidan sarautar Saudiyya ya bayar da sanarwar gayyato shahararren makidi, Armin Van Buuren, zuwa bikin rawa na farko a tarihin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng