Da Bindigar Harbi-Ka-Ruga Muke Fashi Da Makami, Inji wani karamin yaro dan aji biyu a karamar Sakandire
Yan sandar jihar Benue, sun cafke wani karamin yaro dan aji biyu a karamar sakandire mai suna Atoo Aondoana da hannu dumu-dumu a fashin da ake yawan yi a babbar hanyar Makurdi zuwa Alaide.
An kama Aondoana tare da abokin fashin sa Peter Aghande, wanda yake aikin shara a hukumar sojin sama ta kasa wato Nigeria Aiforce dake Makurdi. Ana zargin Aghande da samar da kayan sojojin da suke amfani da su wajan aiwatar da fashin.
KU KARANTA: Kotu ta yankewa wani shahararen jarumin Bollywood shekara 5 a gidan yari
Tun farko dai, an yi zargin yaron dan kasa da shekara 18 na yin amfani da kakin soja wajan yi fashi. Ya kuma amsa laifin da ake zarginsa tare da karin bayanin cewa yana samun kakin sojan ne daga wajan wani mutum.
"Muna amfani da bindigar harbi-ka-ruga ne amma ba da ita aka kama ni ba. Ba ni da makami lokacin da aka kama ni. Ni dalibi ne a makarantar sakandire ta Ikpayong.
"Babana manomi ne kuma ni kadai ya haifa, ba sa tare da mahaifiyata, ta auri wani mutum." In ji Aodoana
Aghande ya bayyana cewa, sojojin ne ke bashi kakin nasu idan sun lalace don ya je ya jefar. Daga bisani yaron ya roke shi ya rinka bashi kakin maimakon jefar da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng