Sankarau: Mutane 10 sun mutu, an kwantar da wasu da dama a Baburan jihar Jigawa

Sankarau: Mutane 10 sun mutu, an kwantar da wasu da dama a Baburan jihar Jigawa

A kalla mutane 10 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwar su yayin da fiye da dozin ke kwance asibiti a bayan bullar cutar sankarau a karamar hukumar Babura dake jihar Jigawa.

Rahotannin da muka samu sun tabbatar da barkewar cutar a kauyukan Ganji, Maulu da Baru dukkansu a karamar hukumar ta Babura.

Wannan rahoto na zuwa ne bayan samun barkewar cutar ta sankarau da tayi sanadiyar yara fiye da goma a karamar hukumar Taura dake jihar ta Jigawa.

Sankarau: Mutane 10 sun mutu, an kwantar da wasu da dama a Baburan jihar Jigawa
Badaru Abubakar; Gwamnan jihar Jigawa

Kazalika rahoto ya bayyana cewar, barkewar cutar wannan karon, ba iya yara ta shafa ba, har da manya.

Mutanen kauyukan sun ce, mutanen da suka kamu da cutar kan yi korafin fama da matsanancin ciwon kai kafin daga bisani su fara amai sannan sai samun labarin mutum ya mutu bayan sa'a 48 matukar ba a hanzarta Kai mutum asibiti ba.

DUBA WANNAN: Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Muhammed Ibrahim, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana cewar tuni aka tura ma'aikatan lafiya kauyukan domin shawo kan annobar.

Karamar hukumar Babura ce mahaifar gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng