Masarautar Daura ta tafka babbar asara da mutuwar Sanata Mustapha Bukar –Mai martaba Sarkin Daura
Mai martaba Sarkin Daura,Alhaji Umar Farouk Umar ya bayyana mutuwar Sanata Mustapha Bukar a matsayin babbar rashi ga masarautar Daura.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Sarki Umar yana fadin haka ne a fadarsa dake garin Daura, inda yace Sanatan Bukar wakili ne mai amince, kuma yace ya taimaka wajen cigaban addinin Musulunci da al’adun gargajiya.
KU KARANTA: Halin mutum jarinsa: Dalilai 3 da zasu baiwa El-Rufai nasara a burinsa na Tazarce a Kaduna
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarki Umar ya kara bayyana Bukar a matsayin mutumi mai saukin kai, wanda ya sadaukar da rayuwarsa don yi ma jama’a bauta, ga shi mai rikon addini, wanda ke ganin mutunci tare da girmama na gaba.
“Dan uwana Mustapha Bukar mutum ne mai kaunar zaman lafiya, wanda yayi tasiri a rayuwar mutane da dama, zamu cigaba da yi masa addu’ar samun rahama, Allah ya azurta shi da aljanna Firdausi.
“Ina mika gaisuwar ta’aziyyata zuwa ga iyalansa, danginsa, abokan aikinsa a majalisar dattawa, gwamnatin jihar Katsina, dama gwamnatin Tarayya gaba ki daya, tabbas gaba dayanmu mun yi babbar rashi.” Inji Sarki Umar Farouk.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng