Hukumar 'Yan sanda ta damko fiye da muggan makamai 70 a garin Kaduna

Hukumar 'Yan sanda ta damko fiye da muggan makamai 70 a garin Kaduna

Da sanadin shafin PM News, mun samu rahoton cewa a ranar Larabar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta jihar Kaduna, ta damko wasu fiye da muggan makamai 70 daga daidaikun mutane da kuma 'yan ta'dda a cikin birni da kewayen jihar.

Kwamshinan 'yan sanda na jihar, Mista Austin Iwar, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da masu ruwa da tsaki da suka hadar da sarakunan gargajiya da kuma kungiyar 'yan farauta ta sa kai.

Hukumar 'Yan sanda ta damko fiye da muggan makamai 70 a garin Kaduna
Hukumar 'Yan sanda ta damko fiye da muggan makamai 70 a garin Kaduna

Iwar wanda ya sakaya wannan makamai dai ya bayyana cewa, hukumar ta na sa ran ci gaba da samun makamanciyar wannan nasara a kullum daga wasu sassa na jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, a karshen mako mai gabatowa za a bayyana wannan makamai domin al'umma su ganewa idanun su kamar yadda shugaban 'yan sanda ya bayyana.

KARANTA KUMA: Yadda cutar hawan jini da ciwon hanta ke yiwa 'yan Najeriya kisan mummuke

Ya tabbatar wa da masu ruwa da tsaki cewa, za aci gaba da jajircewa domin tabbatar da samun zaman lafiya da kuma ci gaba a jihar ta Kaduna.

A na sa jawabin, shugaban kungiyar mafarautan Alhaji Baba Wuro, ya yabawa kwamishinan sakamakon wannan hobbasa da zai wanzar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng