Gwamna Bello ya halarci taro a fadar shugaban kasa cikin sandar guragu
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, cikin sandunan guragu, ya halarci taron gwamnonin jam’iyyar APC da shugaba Buhari da aka yi jiya a fadar gwamnatin tarayya.
Kakakin gwamnan, Kingsley Fanwo, ya bayyana yadda gwamnan ya samu ciwo a kafar sa hart a kai ga likitocinsa sun nade masa kafar da bandeji.
Ya bayyana cewar, gwamnan ya samu raunin ne bayan kafar sat a gurde yayin da yake kokarin saukowa daga mota.
“Gwamnan ya zame ne yayin da yake saukowa daga mota ranar juma’ar da ta wuce, 30 ga wata, hart a kai gay a samu tsagewar kasha a kafar sat a hagu. Likitocinsa sun duba shi, sun nade kafar sannan sun sallame shi,” a cewar Fanwo.
DUBA WANNAN: Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru
“Muna masu godiya ga magoya bayan gwamna da masu yi masa fatan alheri bisa kulawar da suka nuna ga tsautsayin day a samu gwamnan. Mai girma gwamna yana cikin koshin lafiya, kuma zai dawo bakin aikinsa da zarar ya kamala hutun ista.”
Fanwo ya rufe jawabinsa da cewar, “kamar koda yaushe, gwamna Bello na mika sakon fatan alheri ga jama’ar jihar Kogi.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng