Halin mutum jarinsa: Dalilai 3 da zasu baiwa El-Rufai nasara a burinsa na Tazarce a Kaduna
A yayin da zabukan 2019 ke karatowa, yan siyasa na ta yin lissafi tare da warwarewa duk a kokarinsu na neman hanyar da zata dawwamar dasu a farfajiyar siyasar kasar, tun daga shugaban kasa, Yan majalisu har zuwa gwamnoni.
A nan Legit.ng ta yi binciken wasu muhimman alkalumma da ka iya kai gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ga nasara a burinsa na sake tsayawa takarar gwamnan jihar karo na biyu, ma’ana Tazarce.
KU KARANTA: Fitacciyar jarumar Kannywood, Zee Zee ta watsa hotunan Saurayinta suna soyewa
A yan kwanakin nan dai an ji duriyar gwamnan a kafafen sadarwar sakamakon rikicinsa da Sanatocin jiharsa dake majalisar dattawa, kan batun neman umarnin ciyo bashin dala miliyan 350 daga bankin Duniya.
Sai dai duk da wannan akwai wasu abubuwa da gwamnan zai iya amfani dasu wajen yakin neman zabensa a karo na biyu, da suka hada da:
Guguwar Buhari: kamar yadda kowa ya sani akwai wata guguwa da take tasowa a duk shekarar zabe, da aka fi sani da guguwar Buhari, wanda tun a shekarar 2003 da ya fara tsayawa takarar shugaban kasa take yin tasiri a siyasar Najeriya, musamman ma a Arewacin Najeriya.
Don haka kamar yadda gwamna El-Rufai ya sha fada, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi matukar tasiri a zamansa gwamnan jihar Kaduna, kuma duba da kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da Buhari, ana ganin tasirin guguwar nan zata maimaitu a Kaduna.
Ayyukan raya jihar Kaduna: ko a tsakanin yan adawa sun san gwamna El-Rufai katafila ne sarkin aiki, wanann kuwa tun ma kafin shigowarsa siyasa sanannen abu ne, wanda kowa ya shede shi a kai. Sakamakon jihar Kaduna na daga cikin koma baya a tsakanin jihohin Arewa a fannin ayyukan raya jiha, El-Rufai ya debo ayyuka da dama, da suka hada da tituna, gidaje, asibitoci, kwalbatoci, gyaran makarantu, ruwan sha, tsarin aikin gwamnati, samar ma matasa ayyuka da sauransu da dama.
Wadannan ayyuka da dama wadanda ba’a ambata ba zasu saukaka ma Malam yakin neman zabe a kakar zaben bana 2019, kuma dayake jama’a da dama sun shaida ayyukan nan, zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya zarce don su cigaba da sharbar romon dimukradiyya.
Karfin Siyasa: Idan mai karatu zai tuna, mun kawo muku rikicin Malam Nasiru da Sanatocin jihar Kaduna da suka hada da Sanata Hunkuyi da Sanata Shehu Sani, sai dai duk da haka, jam’iyyar APC ta jihar Kaduna da dukkanin shuwagabanninta na yi ma gwamnan biyayya ne.
Haka zalika kantomomi da sauran masu rike da mukaman siyasar jihar, yan majalisun dokokin jihar, da yan majalisun wakilan jihar dukkaninsu suna tare da Malam, don haka shi ke rike da kaso mafi tsoka na yayan jam’iyyar APC, don haka ake ganin ba zai samu matsala ba wajen zama dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng