Na fi kaunar mutanen da za su faɗa min gaskiya komai ɗacinta– Masari ga hadimansa
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari yace zai cigaba da shigar da mutanen da ya san zasu iya fada masa gaskiya komai dacinta cikin gwamnatinsa, inji rahoton Kamfanin dillancin labaru, NAN.
Masari ya bayyana haka ne a yayin rantsar da wani sabon mashawarcinsa, Malam Bashir Ruwan-godiya, tare da wasu sabbin alkalan kotun shari’ar Musulunci na jihar Katsina, Saidu Usman, Muhamamd awal da Mustapha Sani a ranar Talata 3 ga watan Afrilu.
KU KARANTA: Cin zarafin ƙananan yara: Kotu ta garkame wani Mutumi daya kwashe shekaru 7 yana zakke ma ɗiyar matarsa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan na cewa yana jin dadin suka mai ma’ana, kuma a shirye yake ya dauki duk wani shawarar da zata inganta gwamnatinsa. Yace hakan ya bashi damar shugabantar jihar yadda ya dace.
Masari ya bukaci sabbin alkalan da mashawarcin nasa dasu jajirce wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata tare da sanya tsoron Allah a duk lamurransu:
“Gwamnati ta yi nata ta hanyar nada mutanen da suka dace a inda suka dace, ina tuna muku akwai hisabi a lahira da zamu fuskanta. Don haka ina shawartarku da ku ji tsoron Allah a wajen gudanar da aikinku.” Inji Masari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng