Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

- Wata mata mai suna Janet Mohammed ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji bayan sunyi ‘yar hatsaniya

- Mohammed ya bayyanawa manema labarai cewa hatsaniyar sunyi ta ne akan lafiyar jaririnsu dan wata 11

- Mohammed yace saboda ya hanata ta kai yaron Coci ya janyo har sukayi hatsaniyar ta wadda mamnsa ta shiga tsakani

A ranar 3 Afirilu, 2018, wata mata ‘yar unguwar Mandela, a jihar Niger, mai suna Janet Mohammed, ta watsawa mijinta, Mr Alaska Mohammed, ruwan zafi hade da yaji bayan sunyi ‘yar hatsaniya a tsakaninsu.

Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta
Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

Mohammed ya bayyanawa manema labarai na kamfanin dillancin labarai (NAN), cewa hatsaniyar sunyi ta ne a kan lafiyar jaririnsu dan wata 11, saboda ya hanata ta kai yaron Coci ya janyo har sukayi hatsaniyar ta wadda mahaifiyarsa ta shiga tsakani.

KU KARANTA: Kungiyar WANSA ta zabi Buhari a matsayin mamba kwamitin masu bayar da shawara

Bayan mahaifiyata ta shika tsakaninmu ita matar tawa take cewa sai nayi nadamar dukan da nayi mata amma dai ban damu da barazanarta ba. Yace ina cikin cin abinci ina kallon talabijin ta watsa mani ruwan zafin mai hade da yaji”, inji shi.

Mohammed yace an kai kara ga hukumar ‘Yan Sanda na Tudun wada. ASP Muhammad Abubakar yace, duk da matsalar ta tsakanin miji da matace, ta’addanci dai ne kuma duk da cewa mai laifin ta gudu amma duk lokacin muka kamata zamu hukunta ta yanda ya kamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164