Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi wa abokan sa da yaran sa korar kare

Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi wa abokan sa da yaran sa korar kare

- Adam A. Zango yayi wa abokan sa da yaran sa korar kare

- Yace daga yanzu ba shi ba su sakamakon wani sabanin da suka samu

- Ya bar mutum daya ne kacal kawai daga cikin yaran na sa wanda ake cewa Adamu Usher

Kamar dai yadda muke samu daga majiyoyin mu, rahotanni daga jihar Kaduna dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya inda ke zaman tamkar babban gari na biyu da ya tara masu sana'ar fim bayan Kano sun nuna cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa din nan kuma mawaki watau Adam A. Zango ya kori yaransa baki daya.

Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi wa abokan sa da yaran sa korar kare

Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi wa abokan sa da yaran sa korar kare

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana ranar auren ta

Mun samu cewa jarumin haka zalika cikin fushi ya kori kuma dukkan abokan sa da ke tarayya da shi inda ya bayyana cewa daga yanzu ba shi ba su sakamakon wani sabanin da suka samu.

Legit.ng ta samu cewa sai dai bayanan da muke samu daga wasu na kusa da jarumin na nuni ne da cewa ya bar mutum daya ne kacal kawai daga cikin yaran na sa wanda ake cewa Adamu Usher.

Da muka kara zurfafa bincike, mun samu cewa babban dalilin da ya sa shahararren mawakin ya yanke wannan danyen hukuncin shine saboda a cewar ta sa yaran nasa ba su kare mashi mutuncin sa suna bari ana zagin sa duk da cewa yana biya musu bukatunsu daidai gwargwado.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel