Jami’an rundunar Yansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane guda 5 a Taraba
Jamian rundunar Yansandan Najeriya, reshen jihar Taraba sun bindige wasu barayin mutane guda biyar akan babbar hanyar Bali zuwa Jalingo, a jihar Taraba, inji rahotn Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar Taraba, David Akinremi ne ya bayyana haka a yayin taron manema labaru daya gudana babban birnin jihar Taraba, Jalingo a ranar Lahadi, 1 ga watan AFrilu.
KU KARANTA: Wasu barayin mutane sun yi garkuwa da wani babban Limami a Kebbi, amma fa addu’a ta yi aiki akansu
Kwamishina David yace miyagun mutanen da Yansanda suka kashe sun dade suna addaban jama’an kananan hukumomin Balo, Gassol da Gashaka, ta hanyar kai musu hare hare babu ji babu gani.

Kwamishinan ya cigaba da cewa sun kwato muggan makamai da suka hada da bindigar AK 47, bindigar ‘Pump action’ da wata karamar bindiga, sai kuma dimbin alburusai, duk daga hannun yan bindigan.
A wani labarin kuma, rundunar Sojojin kasar Najeriya ta bakin Kaakakinta, Birgediya Texas Chukwu ya sanar da kama wasu miyagun mutane daga kabilun jihar Taraba a ranar Lahadi 31 ga watan Maris, a garn Mayo Ndaga.
Texas ya bada sunayen mutanen a kamar haka Amos Titus, Palat Jafainal, Kingsley Benson, Rapheal Abel, da Yusuf Abdulkareem, dukkaninsu yan kabilar Kaka, kuma an same du da bindiga, na’urar bada wuta, keken dinki da kuma kwanukan rufin gida.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng