Wasu barayin mutane sun yi garkuwa da wani babban Limami a Kebbi, amma fa addu’a ta yi aiki akansu

Wasu barayin mutane sun yi garkuwa da wani babban Limami a Kebbi, amma fa addu’a ta yi aiki akansu

Rundunar Yansandan jihar Kebbi ta sanar da sako babban limamin Senchi dake karamar hukumar Danko/Wasagu, mai suna Alhajo Mode Senchi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 18 ga watan Maris ne dai yan bindigan suka sace Shehin Malamin, inda suka yi garkuwa da shi, wanda wannan ne karo na biyu da ake sace Malamin, kamar yadda rundunar Yansandan ta bayyana.

KU KARANTA: Ajali yayi kira: Ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi awon gaba da wasu daliban sakandari

Kwamishinan Yansandan jihar, Ibrahim Kabiru ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 1 ga watan Afrilu, a birnin Kebbi, inda yace: “A ranar 18 ga watan Maris ne muka samu rahoton satar Alhaji Mode, babban limamin garin Senchi, amma mun ceto shi daga hannunsu a ranar 28 ga watan Maris, kuma yana cikin koshin lafiya.”

Sai dai kwamishinan ya tabbatar da cewar an taba sace Limamin a shekarar 2017, har sai da ya biya kudin fansa na naira miliyan 13, kafin nan suka sako shi, amma yayi ikirarin ba’a biya ko sisi ba a wannan karo.

Haka zalika, kwamishinan ya bayyana cewar sun kama wasu yan fashi da makami guda uku a ranar 28 ga watan Maris, dauke da bindigu guda uku, inda yace a yanzu suna kan gudanar da binciken kwakwaf akansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng