‘Yan ta’adda sun hallaka mutane a Borno bayan wani aran-gama da Sojoji

‘Yan ta’adda sun hallaka mutane a Borno bayan wani aran-gama da Sojoji

- Sojojin Najeriya sun yi ram da wasu ‘Yan ta’adda na Boko Haram a Borno

- Nan take aka buda masu wuta amma ayi rashin wasu Bayin Allah a harin

- Rundunar Sojin kasar ta Operation lafiya Dole ce ta bayyana wannan jiya

Duk da cewa Gwamnatin Najeriya tayi ikirarin gamawa da ‘Yan ta’addan Boko Haram, mun ji cewa ‘Yan Boko Haram din sun yi barna a Jihar Borno yayin da ake cikin hutun bukukuwan Easter bayan Sojoji sun buda masu wuta.

‘Yan ta’adda sun hallaka mutane a Borno bayan wani aran-gama da Sojoji
Sojoji sun kashe wasu 'yan kunar-bakin-wake a Borno

An kashe wasu ‘Yan ta’adda na Boko Haram lokacin da su kayi kokarin maidawa Sojoji wuta. Bayan hakan an samu kayan da ‘Yan ta’addan ke amfani da su wanda su ka hada da wata katuwar mota da ma man fetur da kuma wasu manyan makamai.

KU KARANTA: Mutane 3 da aka tunani za su maye gurbin Oyegun

Wani babban Jami’in yada labarai na Sojojin ‘Operation Lafiya Dole’ Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa an kashe Sojojin Boko Haram yayin da su ke kokarin shigowa cikin Gari bayan an fatattako su daga cikin Dajin Sambisa kwanaki.

Duk a cikin ‘dan lokacin nan, mun ji cewa mutane 3 ne su ka auka lahira a wannan harin da aka kai a Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno inda ‘yan ta’addan su ka raunata mutane akalla 18 wanda aka wuce da su asibiti nan-take domin a duba su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng