'Yan sanda sun kama bindigogi 35 da alburusai 222 a jihar Nasarawa
- ‘Yan Sandan jihar Nasarawa sun gano bindigogi 35, da kuma alburusai 222 a takanin kana nan hukumomi 13 na jihar
- Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Mr. Bello Ahmed ya tabbatar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai
-Yace an bawa jami’an ‘Yan Sandan umurni daga helikwatar hukumar, don samar da kwanciyar hankali ga mutanen kasa
‘Yan Sandan jihar Nasarawa sun gano bindigogi 35, da kuma alburusai 222 a tsakanin kananan hukumomi 13 na jihar, cikin kauyuka 18 dake tasowa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Mr. Bello Ahmed, ya tabbatar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Lafiya.
Ya kuma kara da cewa hukumar ta yan sanda ta dukufa wajen kawo karshen hare-haren da yan daba kai kaiwa a wasu sassan jihar.
KU KARANTA: Shugabanin da suka mulki Najeriya tun 1999
Yace, “an bawa jami’an ‘Yan Sandan umurni daga helikwatar hukumar, don samar da kwanciyar hankali ga mutanen kasa”.
Kwamishinan yayi bayanin cewa hukumar ta samu nasarar tattara makamai dake boye a wurare dabn-daban, a jihar, sakamakon rahotannin da suka samu. Shugaban ‘Yan Sandan ya kara da cewa, anyi nasarar kama mutane da dama masu amfani da makamai ba tare da izini ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng