Ana murna bako ya tafi: Yan bindiga sun kai wani hari a Kaduna, sun kashe mutum 6
Wasu gungun yan bindiga sun kai hari a kauyen Bakin Kogi dake cikin masarautar kabilar Kanikon a karamar hukumar Jama’a, inda suka kashe mutane shidda tare da jikkata da dama.
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Mukhtar Aliyu ya tabbatar da harin, inda yace ya faru ne da misalin karfe 10 zuwa 11 na safiyar ranar Alhamis 29 ga watan Maris.
KU KARANTA: Ba zamu taba mantawa da badakalar cin hanci da rashawa da ya gudana a zamanin Goodluck ba – Osinbajo
Kaakakin Mukhtar yace yan bindigan su bude wuta ne akan wasu kauyawa dake aikin hakar ma’adanan kasa a Bakin Kogi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar maza hudu da mata guda biyu.
Sai dai Mukhtar yace tuni aka tura jami’an Yansanda kauyen don kare aukuwar harin ramuwar gayya, tare da kwantar da tarzoma a wajen, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun hare haren yan bindiga a kauyukan jihar Kaduna ba, inda ko a ranar Alhamis din sai da aka binne Sojoji guda 11 da yan bindiga suka hallaka a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng