Gwamnan jihar Taraba ya nuna ma Buhari yatsa game da matsalar tsaro data dabaibaye jihar

Gwamnan jihar Taraba ya nuna ma Buhari yatsa game da matsalar tsaro data dabaibaye jihar

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya nuna ma shugaban kasa Muhammadu Buhari yatsa, inda ya zarge Buharin da hannu dumu dumu cikin hare haren da ake kai ma jama’an jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito Ishakun yana cewa shugaba Buhari da hadin kan rundunar Sojin Najeriya ne suka yi sake har jihar Taraba ta shiga halin ni-yasun da ta tsinci kanta a ciki, ta hanyar rashin nuna damuwa game da rahotannin da ake kai musu.

KU KARANTA: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Darius ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakinsa Bala Dan Abu, wanda yace hukumar Soji na sane da barazanar tsaro da ake samu a jihar, hakazalika suna sane da irin ayyukan da Sojoji ke yi, wadanda basu dace ba, amma suka yi kunnen uwar shegu da rahoton.

Gwamnan jihar Taraba ya nuna ma Buhari yatsa game da matsalar tsaro data dabaibaye jihar

Ishaku

Bugu da kari ya zargi Sojoji da hada kai da mayakan Fulani da nufin kai hare hare kan sauran kabilun jihar, inda ya bada misali da wani ziyara da wasu Sojoji suka kai jihar Taraba a shekarar 2016, ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Kaakakin ya cigaba da fadin cewa a shekarar 2016, gwamnan ya aika ma shugaba Buhari wasika, inda a ciki yake mai karin haske game da barazanar tsaro da suke fuskanta, amma Buharin bai dauki wani mataki ba.

Dan Abu yace duk kiraye kirayen da suka yi ga gwmanatin tarayya na cewa rudunonin Sojin kasa, sama da na ruwa su kafa sansanoninsu a jihar ko haka zai magance matsalar tsaron da suke fuskanta, ya ci tura. Don haka suke ganin da gangan ake yi ma jihar Taraba irin wannan kullalliya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel