Dalar shinkafa: An kaddamar da shirin bunkasa noman shinkafa a jihar Borno

Dalar shinkafa: An kaddamar da shirin bunkasa noman shinkafa a jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno da hadin gwuiwar ma'aikatar noma da babban bankin kasa (CBN), ta kaddamar da tsarin dalar shinkafa, a wani shiri na bunkasa harkar noma.

A jiya, Talata, gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya kaddamar da shirin. Wani kamfani, WaI Wanne and sons Ltd, ne zai ke dillancin shinkafar da kananan manoma suka noma a jihar.

Shirin bunkasa noman zai kirkiri wata tsani tsakanin kananan manoma da kuma manyan kamfanonin sarrafa domin inganta harkar nomanta da kuma rage dogaro da shinkafar kasashen ketare.

Dalar shinkafa: An kaddamar da shirin bunkasa noman shinkafa a jihar Borno
Dalar shinkafa: An kaddamar da shirin bunkasa noman shinkafa a jihar Borno

Kamfanin WaI Wanne and sons Ltd ya yiwa kimanin manoma 18,000 rijista tare da samun buhunhunan shinkafa 33,000 da aka yi dala da su yayin kaddamar da shirin jiya a Maiduguri.

DUBA WANNAN: Mata sun yi zanga-zanga bayan sakin wanda ya yiwa matar aure fyade

Jihar ta kaddamar da shirin ne bayan dawowar zaman lafiya jihar, domin inganta rayuwar mutanen jihar da suka koma gonakinsu da kuma samar da aiyuka.

CBN zai samar da rancen kudi ga manoma, yayin da kamfanin WaI Wanne zai sayi shinkafar daga hannun manoman a kan farashin kasuwa.

Gwamna Shettima, a jawabinsa, ya yi godiya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da hukumar sojin Najeriya bisa dagewar su wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas da kuma arewacin Najeriya bakidaya, wanda ba don kokarinsu ba da ba a samu yiwuwar kaddamar da irin wannan shiri mai tasiri ga rayuwar jama'a ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel