Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da shirye shiryen binne Sojoji 11 da suka mutu a Kaduna
Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da kammala shirye shiryen binne jami’an guda 11 da yan ta’adda, yaran Buharin Daji suka kashe a jihar Kaduna, inji rahoton jaridar Premium Times.
Rundunar ta bayyana haka ne a ranar Talata 27 ga watan Maris, inda tace za’a binne mamatan ne a makabartar Sojoji dake jihar Kaduna, kamar yadda mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar, Muhammad Dole ya sanar.
KU KARANTA: 2019: Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da takarar neman kujerar shugaban kasa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Muhamamd yana cewa: “Runduna ta daya na rundunar Sojin Najeriya, zata gudanar da taron binne sojojinta da suka mutu a yayin aikin AYEMP AKPOTUMA, a ranar Laraba 28 ga watan Maris, a Kaduna.”
A kwanakin baya ne dai yan bindiga suka kashe Sojoji 11 a unguwar Kanfanin Doka garin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yayin da suka kai wani harin ramuwar gayya, sakamakon kashe musu shugaba,Buharin Daji.
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna, a karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai ta yi Allah wadai da wannan hari cikin wata sanarwar da ta fitar ta bakin Kaakakinta, Samuel Aruwan a lokacin da lamarin ya faru.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng