Saudiyya ta kai karar kasar Iran gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya
Mahukunta a kasar Saudiyya sun kai karar kasar Iran gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya (MDD).
Kasar Saudiyya ta shigar da korafin ne bisa zargin cewar kasar Iran na bawa kasar Yemen makamai. A cewar kasar ta Saudiyya, hatta makami mai linzami da sojojin kasar Yemen da hadin gwuiwar kungiyar Ansarullah suka harba kasar Saudiyya, kirar kasar Iran ne.
Jakadan kasar Saudiyya a MDD, Abdullahi Al-Mu'ulami, ne ya gabatar da takardar koken gaban kwamitin tare da bayyana cewar har yanzu kasar Iran na cigaba da aike makamai zuwa kasar Yemen.
DUBA WANNAN: Dalilin da ya hana Tinubu halartar taron jam’iyyar APC da Buhari ya kira jiya
Wata jaridar kasar Iran, Trt, ta wallafa cewar, manufar kasar Saudiyya shine saka ragowar kasashen duniya juya baya ga kasar Iran.
A wani labarin na Legit.ng kunji cewar, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na CNN a jiya, Talata, mutum na biyu da ya fi kowa kudi a duniya, wato Bill Gates, ya sake caccakar gwamnatin tarayyar Nigeria kan gazawarta a bangaran ilimi da kiwon lafiya
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng