Katankatana: Rusa wani masallaci da gwamnatin jihar Kebbi tayi ya bar baya da kura
Aikin rusa wani Masallaci dake cikin garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi ya bar baya da kura, tun bayan da jama’an garin suke zargin cewar da gwamnan jihar, Atiku Bagudu ne ya bada umarnin rusa Masallacin.
Wannan Masallaci dai yana kallon babban bankin Najeriya dake birnin Kebbi, a kan Titin Sarki Haruna, kamar yadda wani ma’baocin shafin kafar sadarwar zamani na Facebook Hassan Suleyman Benue Makurdi ya tabbtar.
KU KARANTA: Gwani na gwanaye: An samu ɗalibai masu shaidar digiri mai daraja ta daya daga jami’ar Bayero
Sai dai majiyar Legit.ng ya bayyana cewar sun samu labarin gwamnan jihar ya bada umarnin rushe wannan masallaci ne da wata manufa ta siyasa, musamman duba da cewar ba’a taba samun wani korafi daga jama’a ba dangane da Masallacin.
Majiyar namu bai tsaya nan har sai da ya bada karin hujja game haramcn rushe Masallaci, inda yayi duba ga wata shara’a da babbar Kotun babbar birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci, inda tace babu wanda ya isa ya kori mutane daga gidansu ko wajen ibada har ma ya rushe shi, ko da suna kan haramtaccen fili ne, har sai ya bi ka’idojin da doka ya tanadar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng