An maida makarantun mata na jihar Borno cikin garin Maiduguri da Biu, saboda tabbatar da tsaro
- A lokacin da majiyar mu ta zanta da Kwamishinan Ilimi na jihar Borno, Alhaji Inuwa Musa Kubo akan irin zancen da ake yadawa a ciki da wajen jihar na cewa gwamnatin jihar ta saka an rufe dukkanin makarantun mata dake jihar, kwamishinan ya bayyana matakin da gwamnatin ta dauka maimakon rufe makarantun da ake tunanin ta yi
A lokacin da majiyar mu ta zanta da Kwamishinan Ilimi na jihar Borno, Alhaji Inuwa Musa Kubo akan irin zancen da ake yadawa a ciki da wajen jihar na cewa gwamnatin jihar ta saka an rufe dukkanin makarantun mata dake jihar, kwamishinan ya bayyana matakin da gwamnatin ta dauka maimakon rufe makarantun da ake tunanin ta yi.
DUBA WANNAN: Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya data daina kama masu shan tabar wiwi
A bayanin sa ya ce makarantun jihar duka suna aiki, sai bayan da aka sace 'yan matan Chibok sai gwamnatin jihar ta yanke shawarar ta dauke dukkanin makarantun kwana ta mata ta maida su cikin garin Maiduguri domin tabbatar da tsaro da lafiyar su. Amma jita-jitar da ake yi na an rufe makarantun ba gaskiya bane.
Kwamishinan ya kara da cewar manufarsu a nan ita ce suna so su tabbatar da cewar babu wata makaranta ta 'yan mata a fadin jihar wacce take wurin da babu tsaro. Sannan kuma da zarar an samu ingantaccen tsaro a wasu wuraren za'a mayar da wasu makarantun.
Banda makarantun 'yan matan ma akwai wasu makarantu da yawa da wuraren da suke babu cikakken tsaro, dalilin hakan yasa muka debe su muka maida su wuraren da akwai tsaro.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng