An bankado yadda Kasar Birtaniya ta shigo cikin harkar zaben Najeriya a 2007

An bankado yadda Kasar Birtaniya ta shigo cikin harkar zaben Najeriya a 2007

- An gano yadda Ingila ta shiga harkar zaben Najeriya shekarun baya

- Wani kamfani yayi kokarin hana Shugaban kasa Buhari lashe zabe

- A lokacin Jonathan ma an yi kokarin danne Jam’iyyun adawar kasar

An gano cewa wani babban kamfanin da ya rikida ya zama Cambridge Analytica na Kasar waje yayi wa Najeriya kutse a lokacin zaben 2007 wanda tsohon Shugaban kasa ‘Yaradua yayi nasara.

An bankado yadda Kasar Birtaniya ta shigo cikin harkar zaben Najeriya a 2007
Ingila ta yi kutun-kutun din hana Buhari lashe zabe a baya

Gidan watsa labari na BBC ta rahoto cewa Kamfanin Cambridge Analytica ta shiga cikin harkar zaben kasashen Duniya wanda daga ciki har da Najeriya. Kamfanin yayi wannan danyen aiki ne domin hana Jam’iyyun adawa kai labari lokacin a Najeriya.

KU KARANTA: Kwankwaso ya fara shiryawa zabe mai zuwa a Najeriya

A lokacin zaben 2015 ma dai Kamfanin na Cambridge Analytica yayi yunkurin hana Shugaba Buhari cin zabe lokacin da yayi takara da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kamfanin dai ya kashe makudan kudi amma ba ayi nasara ba.

Gwamnatin Kasar Ingila dai tace ba ta san da labarin ba amma za ayi bincike a kai. Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua yayi nasara dai a zaben na 2007 inda ya doke Muhammadu Buhari na ANPP su Atiku Abubakar na Jam’iyyar ACN.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng