Ma’aikatan Kuros-Riba za su gyarawa Gwamnan Jihar zama
- Ma’aikatan Jihar Kuros-Riba sun ce za su ga karshen Gwamna Ben Ayade
- Kungiyar Ma’aikata dai sun koka da wulakancin da Gwamnan yake yi masu
- Sun bayyana cewa idan ba a kara masu matsayi a ofis ba za a ga danyen aiki
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade sai ya dage kafin ya samu damar komawa kujerar sa a zaben 2019 bayan da Ma’aikatan Jihar su ka taso shi gaba.
Kungiyar WSF ta Ma’aikatan Jihar Kuros-Riba da ke Kudancin Najeriya sun ce za su shirya jama’a domin ganin Gwamna Ben Ayade bai koma kan kujerar sa na Gwamna ba a 2019 idan har bai sake tunani kan wata matsaya da ya cin ma ba.
KU KARANTA: Sule Lamido yace shi kadai ne fa zai iya gyara Najeriya
Ma’aikatan ta bakin Shugaban WSF Mista Savior Akepeyi sun koka da cewa Gwamnan Jihar ya ki karawa mutanen su matsayi a wuri aiki. Mista Akepeyi ya bayyanawa manema labarai wannan ne a Babban Birnin Kalaba kwanan nan.
Kamar yadda Ma’aikatan su ka bayyana, Gwamnan bai da niyyar karawa ma’aikatan su matsayi duk da dadewar su a wurin aiki. Sai da Kungiyar kwadago NLC ta sa baki a baya sannan aka nemi a sulhunta kuma yanzu maganar ta watse.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng