Gaskiyar abin da ya faru kan mutuwar aurena – Fati KK
Fitaciyyar jarumarnan ta Kannywood wacce aka fi sani da Fati KK ta yi cikakken bayani game da mutuwar aurenta.
Kamar yadda kuka sani ana ta yada jita-jitan mutuwar auren jarumar harma da cewa da akayi ta tattara yanata-yanata ta bar garin Kano inda take zaman aure zuwa Kaduna inda mahaifanta suke.
A cewar jarumar, babu shakka ta so zaman aure domin a cewarta da bata so zaman aure da mijin nata ba da bata hayayyafa da shi ba.
Ta ce ta fuskanci kalubale da dama amma ta shanye iyakaci ta zauna ta sha kukanta amma bata taba neman a sake ta ba.
Fati na da yara biyu da mijin nata, ta kuma ce talauci bai taba sa ta yin tunanin rabuwa da wanda take tare ba, sai dai yaan uwan shi sun zarge ta da bijire masa sa don ya bukacin Karin aure.
KU KARANTA KUMA: A kullun ina rayuwa cikin dar-dar – Melaye
Ta ce mijin nata ne ke kokarin bata mata suna a idanun duniya domin shi aga farinsa.
Daga karshe jarumar ta jadadda cewa ba tace bazata taba aure ba amma dai gaskiya ba zatayi aure a nan kusa ba domin a cewarta maza tsoro suke bata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng