Da dawowar PDP, gara Najeriya ta zauna babu gwamnati, inji tsohon jigo a jam'iyyar PDP

Da dawowar PDP, gara Najeriya ta zauna babu gwamnati, inji tsohon jigo a jam'iyyar PDP

- Tsohon jagoran PDP, Sanata Rowland Owie, ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya bazasu bari PDP ta dawo kan mulki ba a 2019

- Yace matsalolin yanzu dake damun Najeriya a yanzu, jam'iyyar PDP ce ta kirkirasu

- Owie, ya kara da cewa, gwamma ace babu wata gwamnati a Najeriya da dai PDP ta dawo mulki a 2019

Tsohon bulaliyar majalisar Dattawa, kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sanata Rowland Owie, yace ‘yan Najeriya baza suyi kuskuren bari PDP ta dawo kan mulki ba a shekarar 2019.

A wata zantawa da yayi da manema labarai na jaridar Vanguard, Owie, wanda mamba ne na majalisar wakilai tsakanin shekarar 1979 da 1983, yace gara ace babu wata gwamnati a Najeriya da dai PDP ta dawo mulki a shekarar 2019.

Da PDP ta dawo mulki, gwamma a zauna babu gwamnati, inji wani tsohon jigo a PDP
Da PDP ta dawo mulki, gwamma a zauna babu gwamnati, inji wani tsohon jigo a PDP

KU KARANTA: An kori ASP na 'Yan sanda, an kuma yiwa wani murabus

Legit.ng ta ruwaito cewa, yace matsalolin yanzu da Najeriya ke fuskanta a yau, tsohuwar jam’iyyar dake mulki ce ta kirkirasu.

Manyan jam’iyyar sune suka kawo almundahana a cikin mulkin. Lokacin da PDP ta karba mulki kamfanin jirgin Najeriyan Airways na aiki, Aladja na aiki, Ajaokuta na aiki, kamfanin sikari na Basita na aiki, NITEL na aiki.

A takaice lokacin da muna Majalisa, NITEL nada sama da N2.4bn a asusun ajiya, basa rancen kudi don su biya albashi. Amma PDP tazo ta siyar da duk wadannan hanyoyin kasuwanci, wanda a har zuwa yau ba wanda ko mutum daya cikin ma’aikatan kamfanonin da aka biyashi kudinsa na sallama". inji shi.

Bayan wannan, Legit.ng ta ruwaito daga jaridar Daily Trust ta nuna cewa kungiyar siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cigaba da aiki. Duk da dai shugaban kasar bai bayyana shawararsa ba a kan cigaba da mulki a shekarar 2019, hakan zai iya yiwuwa idan har maganar ta fito ne daga bakin shugaba Buhari. Idan har ya amsawa fadar shugaban kasa cewa zai tsaya takara a karo na biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164