Za'a samar da 'Yan sanda hudu ga kowacce makaranta a jihar Borno don inganta tsaro - Sifeta Idris
- Sifeta Janar na Hukumar Yan sandan Najeriya ya yi hubbasa wajen kare rayuka da lafiyar daliban makarantu a yankin arewa maso gabashin kasar nan
- Hakan ne ya sa Sifeta Janar, Ibrahim Idris ya bayar da umurnin girke jami'an yan sanda guda 4 a kowanne makarantar sakandire a jihar Borno
- Idris ya roki dalibai da mahukunta makarantun su bayar da hadin kai ga jami'an yan sandan da za'a turo makarantun
Sifetan Janar na hukumar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya tabbatar wa dukkan makarantun da ke yankin arewa maso gabas da ke fuskantar barazana daga Boko Haram cewa za'a samar da yan sanda da zasuyi gadin makarantun.
Shugaban Yan sandan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma'a, 23 ga watan Maris yayin da ya kai ziyara Kwallejin Gwamnati da kuma Kwallejin Mata na Maiduguri.
Idris ya ce Hukumar Yan sandan ta lashi takobin kawo karshen garkuwa da mutane da akeyi a yankin inda ya bayyar da sanarwan cewa za'a girke yan sanda hudu a kowanne makaranta amma kwallejin gwamnatin na Yelwa za'a basu yan sanda 10.
DUBA WANNAN: Buhari ya lashi takobin ladabtar da wadanda sukayi sakaci aka sace 'yan matan Dapchi
Ya kuma yi kira ga dalibai da mahukunta na makarantun su bawa yan sandan da za'a turo makarantun su hadin kai kuma kar suyi kasa a gwiwa wajen kai musu rahoton duk wani mahalukin da basu yarda da wasu al'amuran sa ba.
Shugaban Yan Sandan kuma ya shawarci daliban makarantar da su guji aikata duk wani abu da zai jefa rayuwar su cikin matsala a nan gaba. Ya kuma tallafa wa kwallejin gwamnati na Maiduguri da buhunnan shinkafa 20 da sa guda daya.
A jawabin da sukayi, shuwagabanin makarantun Kwallejin Gwamnati, Mr. Abba Gana da kuma Hajia Bintu Abakura na kwallejin Mata na Maiduguri sun yaba da kokarin shugaban hukumar na Yan sanda kuma sunyi alkawarin bayar da hadin kai don dawo da tsaro a yankin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng