Za a tsige shugaban kasar Zambia Edgar Lungu
- 'Yan Jam'iyyar adawa na kasar Zambia sun gabatar da wani kudurin doka a zauren majalisar kasar da nufin a cire shugaban kasar Edgar Lungu
- 'Yan majalisun sunce sun dauki niyyar cire shi dinne bisa zargin shi da suke da cin hanci da rashawa da kuma rashin kwarewa akan aiki
'Yan Jam'iyyar adawa na kasar Zambia sun gabatar da wani kudurin doka a zauren majalisar kasar da nufin a cire shugaban kasar Edgar Lungu.
DUBA WANNAN: An rage kudin sadaki a Jamhuriyyar Nijar
Kimanin kashi uku cikin kashi hudu na mambobin adawar karkashin jam'iyyar United Party of National Development sune suka sanya hannu akan kudurin da suka gabatar, wanda suka mikawa shugaban majalisar a ranar Alhamis dinnan data gabata.
Manya daga cikin wanda suka sanya hannu akan kudurin sun hada da tsofaffin ministoci da suka yi mulki a baya irinsu Chishimba Kambwili da Harry Kalaba, wanda su din mambobin jam'iyya mai mulki ne a yanzu.
'Yan majalisun sunce sun dauki niyyar cire shi dinne bisa zargin shi da suke da cin hanci da rashawa da kuma rashin kwarewa akan aiki.
Sai dai kuma kakakin shugaban kasar yayi watsi da maganar ta su.
A yanzu haka dai harkokin siyasar kasar Zambia sunyi tsamari, duk kuwa da cewa ba za sake yin zaben shugaban kasa ba sai shekarar 2021.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng