Yadda Sardauna ya nada ni Minista ina ‘Dan shekara 30 – Danburam Jada
Abdullahi Danburam Jada Dattijo ne kwarai wanda ya sha miya yayi hira da Jaridar Daily Trust inda ya bayyana yadda ya zama Minista a Jamhuriya ta farko ba tare da ya nema ba. Kafin nan ‘Dan Majalisa ne a karkashin Jam’iyyar NPC.
Danburam Jada ya zama ‘Dan Majalisa ne a 1958 duk da a lokacin yana mai Garin Jada wanda a lokacin tana kasar Kamaru kafin yayi kokari na a shigo da ita cikin Yankin Najeriya. Daga baya ne aka nada shi Minista a kasar.
A hirar da yayi da Daily Trust, yace bai taba sanin cewa za a nada sa Minista ba kurum sai Lamidon Adamawa a lokacin ya fada masa cewa Sardauna na neman sa. Ko da yaje, sai aka ce zai zama Ministan dabbobi nan take.
KU KARANTA: Shugaban Kasar Nijar ya kawowa Shugaba Buhari ziyara
Wannan Dattijo yace a lokacin Sardauna duk da yayi kokarin ganin ‘Yan Arewa ne ke aiki a Yankin, ba ayi amfani da son rai ko son kai ba kuma ba a raba tsaki tsakanin ‘Dan talaka da yaran manyan kasa ba a wancan lokaci.
Bayan yayi Ministan dabbobi, Danburam yayi aiki a Hukumar PCC na karbar korafin Jama’a tare da Dan Masanin Kano. Danburam yace lokacin da ‘Dan Masani ya cika bai da lafiya, amma dole zai je Kano domin yayi ta’aziyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng