Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Zamfara, ya gana da sarakunan gargajiya da shugabannin jama'a

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Zamfara, ya gana da sarakunan gargajiya da shugabannin jama'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Zamfara a yau, Alhamis, a cigaba da rangadin jihohin dake fama da kalubalen tsaro a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Buhari da tawagar sa sun dira a jihar da misalin karfe 10:40 na safiyar yau bayan tashinsu daga filin jiragen sama na Umaru Musa 'Yar'Adua dake jihar Katsina.

Gwamnonin jihohin Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, takwaransa na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, shugabannin addini da sarakunan gargajiya na daga cikin tawagar da suka karbi shugaban kasa a bayan saukar sa.

Kazalika shugaba Buhari ya duba dakarun sojin sama da su ka yi masa faretin ban girma.

anzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Zamfara, ya gana da sarakunan gargajiya da shugabannin jama'a
Shugaba Buhari ya isa jihar Zamfara, ya gana da sarakunan gargajiya da shugabannin jama'a

A yayin ziyarar shugaba Buhari zai gana da sarakunan gargajiya da ragowar masu ruwa da tsaki a harkokin jama'a a jihar domin jajanta ma su irin asarar rayuka da ta dukiya da aka yi a jihar sakamakon hare-haren ta'addanci.

Jihar Zamfara na daga jihohin da aka samu asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon aiyukan ta'addanci, musamman fashi da makami.

DUBA WANNAN: Laifin kisa: An yankewa wani saja hukuncin kisa ta hanyar rataya

A wani hari da aka kwanannan a karamar hukumar Zurmi ta jihar, a kalla mutane 50 aka kashe.

Cikin kwanakinnan nan aka kashe wani shugaban kungiyar masu tayar da hankula a jihar da ake kira Buharin daji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng