Shugaba Buhari ya ki sa hannu a yarjejeniyar da Kungiyar Kasashen Afrika ta shriya

Shugaba Buhari ya ki sa hannu a yarjejeniyar da Kungiyar Kasashen Afrika ta shriya

- A baya an yi da Najeriya za ta shiga cikin sabon tsarin kasuwancin Afrika

- Shugaba Buhari ya sabawa maganar Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

- Sai dai yanzu Shugaban kasar yace ba za su yi garajen sa hannu ba tukuna

Mun samu labarin ainihin abin da ya sa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ki zuwa kasar Rwanda kwanaki wajen yarjejiniyar kasuwancin da kasashen Afrika watau AU su ka shirya. A da dai an shirya cewa Najeriya za ta shiga cikin yarjejeniyar.

Magana biyu: Najeriya ta ki sa hannu a yarjeniyar da Kungiyar Kasashen Afrika ta shriya
Magana biyu: Najeriya ta ki sa hannu a yarjeniyar da Kungiyar Kasashen Afrika ta shriya

Shugaban kasar ya bayyanawa Majalisar Ministocin sa a taron jiya dalilin da ya sa bai je Birnin Kigali kamar yadda aka shirya a makon jiya ba. Shugaba Buhari yace bai gama yin na’am da sabon tsarin kasuwancin da aka bullo da shi na kasashen Afrika ba.

KU KARANTA: Shugaban APC Oyegun yana ganawa da manyan Majalisa

Muhammadu Buhari yana tsoron cewa idan ya sa hannu a sabuwar yarjejeniyar da aka yi Najeriya na iya samun kan ta cikin matsala musamman yanzu da ake kokarin ganin ‘Yan kasuwan gida sun bunkasa don haka Shugaban kasar yace ba zai yi garaje ba.

Yanzu dai Shugaba Buhari ya sa Ministoci 5 da kuma babban bankin kasar da sauran hukumomi da su duba fa’idar sabon tsarin da AU ta kawo da kuma irin tasirin da zai yi wa Najeriya kafin ya dauki mataki a kai nan da mako biyu kamar yadda Femi Adesina ya bayyana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng