An kama tsohon kwamishinan Kwankwaso da Kaftin din soji mai ritaya bisa zargin yunkurin tayar da husuma a Kano
- An kama tsohon kwamishinan Kwankwaso da Kaftin din soji mai ritaya bisa zargin yunkurin tayar da husuma a Kano
- Jami'an hukumar DSS a jihar Kano sun cafke wani tsohon kaftin a hukumar soji bisa zarginsa da yunkurin tayar da rikici a jihar.
- Kokarin jin ta bakin jami'an hukumar DSS a jihar Kano ya ci tura
Kaftin din mai ritaya da ba a ambaci sunansa ba ya amsa cewar tsohon kwamishinan albarkatun ruwa a jihar Kano, Dakta Adamu Yunusa Dangwani, ya bashi kwangilar dagulawa gwamnatin jihar lissafi tare da bayyana cewar ya biya shi miliyan N1.5m somin tabi.
PRNigeria ta rawaito cewar yanzu haka an tafi da tsohon kaftin din Abuja domin zurfafa bincike, yayin da aka kama tsohon kwamishina Dangwani a filin tashin jirage yana kokarin yin bulaguro zuwa kasar waje.
DUBA WANNAN: Sakin 'yan matan Dapchi: PDP ta mayar da martani, ta ce ba zata taba yafewa ba
Gwamnatin jihar Kano ta taba kama tsohon kwamishina a shekarar 2016 bayan ya yi yunkurin yin wani taron gangamin siyasa na nuna adawa ga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje amma an sake shi.
Kokarin jin ta bakin jami'an hukumar DSS a jihar Kano ya ci tura.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng