An kashe maciji ba’a datse kansa ba: Sojoji sun yi artabu da yaran Buharin Daji a jihar Kaduna, sun kashe da dama

An kashe maciji ba’a datse kansa ba: Sojoji sun yi artabu da yaran Buharin Daji a jihar Kaduna, sun kashe da dama

Wasu yan bindiga dake biyayya ga tsohon shugaban yan bindigar dake addabar yankin jihar Zamfara, Kaduna, Kano, Katsin da sakkwato, da aka kashe a kwanakin baya, Buhari Daji, suna cigaba da kai hare haren ramuwar gayya.

Da safiyar ranar Laraba 21 ga watan Maris ne aka samu rahoton yan bindigan sun far ma kauyen Doka, dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka tarar da Sojojin a cikin damara, daga nan akai ta fafatawa, har sai da suka tsere, tare da kowanni bangare ya samu rashi.

KU KARANTA:

Fitaccen dan jaridan nan, Ibrahim Sheme ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace wani babban jami’in gwamnatin tarayya mazaunin garin Birnin Gwari ne ya sanar da shi labarin wannan harin.

Majiyar Legit.ng ya bayyana cewar da misalin karfe 10 na daren ranar Talata 20 ga watan Maris ne yan bindigan kimanin su 120 sua dira garin Birnin Gwari akan Babura dauke da muggan bindigu, inda suka fara yada zango a kauyen Maganda, suka jikkata yan sintiri guda 9.

A hanyarsu ta zuwa Kampanin Doka ne suka tarar da jami’an Sojojin Najeriya, tare da wasu matasan garin Dokan inda suka yi artabu da yan bindigan, tare da karkashesu da dama kamar kiyashi, yayin da sauran suka tsere da raunuka daban daban.

Sai dai majiyar ya tabbatar da cewar manyan garin Birnin Gwari sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna, tare da sauran hukumomin tsaron jihar game da yiwuwar wannan harin, amma suka yi watsi da shi ta hanyar kin daukan matakin da ya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng