Zan zama halifan mahaifina - Dan Marigayi Gaddafi
Dan Marigayi Gaddafi, tsohon shugaban kasar Libiya, ya ce idan ya hau mulkin kasar zai cigaba da aiyukan da mahaifinsa ke yiwa kasar kafin mutuwar sa.
Wani mataimaki ga Saiful Islam mai suna Aiman Abu Ras, ya bayyana cewar, dan marigayin na cikin kasar Libiya cikin koshin lafiya tare da bayar da tabbacin cewar zai tsaya takarar shugabancin kasa a zaben kasar da za a gudanar nan gaba.
Ya kara da cewar, manufar Saifu ita ce dawo da zaman lafiya kasar Libiya tare da hada kan mutanen kasar. Kazalika, ya bayar da tabbacin cewar Saifu zai zama magajin mahaifinsa ta fuskar gudanar da aiyuka ga jama'ar kasar.
KARANTA WANNAN: Za a cashe a kasar Saudiyya, an gayyato wani fitaccen DJ daga Turai
A shekarar 2011 ne aka yankewa Saifu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa zarginsa da aikata laifukan yaki da rura wutar rikici a yayin da ake kokarin hambarar da mahaifinsa daga kan mulki.
Saifu ya kare wa'adinsa a gidan yari a watan Yuni na shekarar bara, 2017.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng