Kamfanin NPPC ta ce zata haka rijiyoyin mai guda hudu a tafkin Gongola
- Hukumar NNPC ta ce zata haka rijiyoyin mai guda hudu a Gongola a cikin wannan shekara
- Mai Kanti Baru ya ce za a cigaba da neman mai a Tafkin Chad idan zaman lafiya ya dawo yankin
Kamfanin NNPC ta ce, ta shirya haka rijioyiyin mai da iskan gas guda hudu a tafkin Gongola a cikin shekara 2018.
NNPC ta ce zata fara haka rijiyoyin tafkin Gongola yayin da take jiran dawowar zaman lafiya a Tafkin Chad.
Shugaban hukumar NNPC ,Mai Kanti Baru, ya sanar da haka a ranar Alhamis a lokacin da ake bashi wata lamabar yabo a jihar Kano.
KU KARANTA : Mutuwar Buharin Daji : Har yanzu kashe kashe bai tsaya ba a jihar Zamafara
Tun a shekara 2016 hukumar NPPC ta sanar da kudirin ta neman danyen man fetur a yankin Gongola.
Maikanti Baru ya bayyana takaicin sa akan harin da mayakan kungiyar Boko haram suka kai malaman jami’an Maidugri da suke je neman mai a jihar Borno a shekara da ta gabata.
Dannan wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng