Ta dabo tumbin giwa, Ko da mai kazoo an fi ka: Cikin ajin da yafi yawan dalibai a kafatanin makarantun Najeriya (Bidiyo)

Ta dabo tumbin giwa, Ko da mai kazoo an fi ka: Cikin ajin da yafi yawan dalibai a kafatanin makarantun Najeriya (Bidiyo)

Makarantar Firamari dake unguwar Rimin Kebe, a cikin karamar hukmar Ungogo na jihar Kano ta ciri tuta a kafatanin Najeriya wajen yawan dalibai, inda a yanzu haka take da wani aji dake dauke da dalibai dari hudu da casa’in da tara, 499!

Jaridar Daily Najeriya ce ta binciko wannan aji a ranar Talata 20 ga watan Maris, inda aka jiyo daliban na amsa lambarsu da harshen Hausa a lokacin da Malamarsu ta tambayesu; “Ku nawa ne a ajin nan?” inda suka amsa gaba daya “Dari hudu da casa’in da tara.”

KU KARANTA: Rayuwarmu na cikin mummunar hadari, a kawo mana agaji – Inji Fulanin jihar Taraba

Majiyar Legit.ng ta ruwaito anyi haka ne a gaban sabon shugaban karamar hukumar Ungogo yayin da ya kawo ziyarar gani da ido makarantar.

Idan za’a tuna, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya daura tubulin gina wata sabuwar makarantar Firamari a unguwar Darmawan da zata dauki kimanin dalibai 21,960, a inda ya tabbatar da cewar jihar Kano na da adadin daliba miliyan uku a makarantun gwamnati.

“A yanzu haka muna da dalibai sama da miliyan uku, wanda adadinsu yafi yawan wasu jihohi gaba daya, hakan ya sanya kujeru da tebura, azuzuwa da sauran kayan karatu sun yi karanci, don haka hakkinmu ne mu sauke wannan nauyi ta hanyar shawo kan matsalar.” Inji Ganduje.

Gwamnan ya bayyana cewar sun ware naira biliyan 2.2 don kashewa a makaratun firamarin jihar a wajen gina sabbin azuzuwa hawa biyu guda 61, ofisoshin malamai, samar da kujeru da tebura, littafai da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng