Rayuwarmu na cikin mummunar hadari, a kawo mana agaji – Inji Fulanin jihar Taraba
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin Arewa maso gabas, Mafindi Danburam ya bayyana cewa Fulani na cikin halin tsoro, fargaba da firgici, don haka yayi kira ga babban sufetan Yansanda ya kawo musu dauki.
Jaridar The Cables ta ruwaito Mafindi ya bayyana haka ne a ranar Talata 20 ga watan Maris, inda ya zarge gwamnan jihar Taraba, Darisu Ishaku da nuna halin wariya da son kai a tsakanin al’ummar jihar.
KU KARANTA: Kwararan hujjoji guda 5 da zasu kai Buhari ga nasara a zabukan 2019
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mafindi yana bayyana mamakinsa da yadda gwamna Darisu ke nuna bambamci a tsakanin Fulani da sauran kabilun jihar, inda ya zargi gwamnan da nuna halin ko in kula a duk lokacin da aka kashe Fulani.
Shugaba Mafindi yace Fulani basa iya tafiya daga gari zuwa gari a jihar Taraba ba tare da sun nemi rakiyar jami’an Sojojin Najeriya ba; “Bamu da wani kyakkyawar yakini a tare da gwamnan, saboda yadda yake nuna Fulani ne ke da laifi a duk lokacin da aka kai wani hari a jihar.
“Har yanzu Fulani kadai ake kamawa da laifin kai hare hare, bayan kuma mu aka fi kashe a jihar nan, a yanzu haka duk wani Fulani dake garin Ussa ko Takum bai isa ya yayi tafiya ba har sai ya nemi rakiyar Sojoji.” Inji Mafindi
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng