Wani jami'in dan sanda ya harbe Soja ana tsaka da muhawara a jihar Delta

Wani jami'in dan sanda ya harbe Soja ana tsaka da muhawara a jihar Delta

Wani jami'in dan sanda mai tsare iyaka ta kamfanin man fetur na Shell ya diga dalma ta harsashin bindiga kan wani Soja a yankin Odimodi na karamar hukumar Burutu dake jihar Delta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da wata rashin jituwa ta shiga tsakanin mazajen biyu.

Wata majiyar rahoto mai karfi ta bayyana cewa, jami'an biyu sun shiga tayar da jijiyoyin wuya ne a sakamakon cacar baki da barke a tsakanin su wadda ba bu masaniya akan musabbabin ta.

Rahoton ya ci gaba da cewa, bayan 'yan dakikai kadan ana tsaka da cacar baki sai sautin fitar harsashi ne kurum ya tashi.

Majiyar rahoton ta kara da cewa, jami'in dan sandan ya ci gaba da harba harsashai saman iska domin baza mutane bayan ya shekar da Sojan kuma ya yi awon gaba da makamin sa.

KARANTA KUMA: Bincike: Jerin jihohi 8 mafi kantar bashi a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'an rundunar hadin gwiwar sun dirafafi wurin da wannan lamari ya afku kuma suka killace gawar jami'in Soja.

Wani shugaba na yankin da bai bukaci a bayyana sunan sa ya tabbatar da afkuwar wannan lamari, inda ya ce al'ummar yankin sun shiga cikin firgici da dimuwa dangane da abinda ka iya biyo baya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin tarayya da bayyana dalilin da ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fasa fita zuwa kasar Rwanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng