Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

Shahararriyar jarumar nan kuma tsohuwar fuska a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood watau Aina'u Ade ta bayyana cewa kawo yanzu dai ba ta da wani tsayayye dake neman ta da aure don haka har yanzu ba ta tsaida lokacin auren na ta ba.

Haka zalika jarumar yayin da ta ke zantawa da wakiliyar majiyar mu, ta kara da cewa "shi aure abu ne na Allah, duk lokacin da Allah ya kawo shi ko ka yi niyya ko ba ka yi niyya ba za ka yi shi ne".

Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta
Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

KU KARANTA: Babban malamin addini ya shiga takarar tikitin Gwamna a Najeriya

Hajiya Aina'u Ade wadda ta shahara a masana'antar a shekarun baya ta yi wadannan bayanan ne a yin da ta ke zantawa da wakiliyar majiyar mu inda take ba da an sa akan wasu lamurra na rayuwar ta.

Har ila yau da aka tambayi jarumar ko meye kabilar ta ta ayyana cewa ita bayarabiya ce amma kuma cikakkiyar 'yar garin Kano don kuwa a nan ne aka haife ta har ta gairma.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa ita ta taba aure har ma ta na da 'ya'ya biyu yanzu haka amma ta rabu da tsohon mijin ta.

Daga karshe kuma Hajiya Aina'u ta ba sauran 'yan fim din musamman ma mata da suka shigo masana'antar daga baya da su rike sana'ar su da muhimmanci sannan su kuma kare kan su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng