Allah ya yiwa shugaban makarantar sakandire mafi dadewa a aiki rasuwa
Tsohon kwararen malamin makaranta kuma limamin darikar katolia, Rabarand Fada Jeremiah Dermot O'Connell ya rasu a kasar sa ta haihuwa na jamhuriyar Ireland bayan ya kammalla aikin koyarwa a Najeriya na tsawon shekaru fiye da 50 a matsayin shugaban makaranta.
Rahotanni da suka fito daga Kasar ta Ireland sun tabbatar da cewa ya rasu ne a safiyar Laraba 14 ga watan Mayu na 2018.
Marigayi O'Connell yana da shekaru 85 a duniya lokacin da ya yi murabus daga matsayin sa a shugaban makarantar sakandire a jihar Neja sannan ya koma kasar su a bara.
KU KARANTA: An damke wani mutum da ya yi wa diyar sa 'yar shekaru 14 ciki
Ya dai iso Najeriya ne a shekarar 1967 a matsayin mishan kuma ya fara aiki ne a Cocin darikar Katolika da ke Calabar kafin daga baya ya koma jihar Neja inda ya kama aiki a matsayin shugaban makarantar sakandire na gwamnati da ke Minna.
Kafin barin sa Najeriya, masarautar Minna karkashin jagorancin Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ta karama shi da sarautar Jagaban Ilimin Minna inda aka gudanar da wata takaitacen liyafa a fadar.
Marigayin ya shahara tsakanin iyayen yara da sauran malamai a jihar ta ba jihohin da ke makwabtaka da jihar inda al'umma suka bayyana shi a matsayin mutum mara kasala da kuma hali na gari wanda ke bayar da gudunmawa wajen tarbiyantar da yara.
A tsawon rayurwar sa a Najeriya, O'Connell ya koyi harsunan Hausa, Nupanci da Gbagyi. Daya daga cikin abinda al'umma za su tuna dashi shine yadda yake iya tuna sunayen dukkan dalibansa da kuma yadda ya ke bayar da gudunmawa wajen inganta rayuwar su.
O'Connell kuma ya samu karamawa na kasa ta MFR daga gwamnatin tarayya tare da ma wasu karamawar daga gida da kuma kasashen waje. Gwamnatin jihar ta Neja ta karama marigayin ta hanyar sanya wa makarantar sunnan sa.
A wata jawabi ya yi a watan Maris na bara, dan majalisar jihar Neja, Honarabul Ahmed Marafa ya ce malamin addinin ya kafa tarihi a duniya kasancewar sa malamin makarantar da yafi kowa dadewa a aiki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng