Tonon silili: Osinbajo ya bayyana yadda aka yi cogen $3bn a wasu kwangiloli karkashin mulkin Jonathan

Tonon silili: Osinbajo ya bayyana yadda aka yi cogen $3bn a wasu kwangiloli karkashin mulkin Jonathan

Kimanin Dalar Amurka biliyan uku, $3bn, su ka bata a wata yarjejeniyar kwangila tsakanin hukumomin NNPC da NPDC a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ne ya bayyana haka yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da zuba jari a fadar gwamnatin tarayya ta Villa a jiya.

Osinbajo ya ce adadin kudin ya ninka adadin kudin dake lalitar gwamnatin tarayya fiye da sau goma.

Tonon silili: Osinbajo ya bayyana yadda aka yi cogen $3bn a wasu kwangiloli karkashin mulkin Jonathan
Farfesa Yemi Osinbajo

"Babu yadda za a yi a sace adadin irin wadannan makudan kudade a ce tattalin arzikin kasa ba zai shiga matsala ba. Dole mu fada, dole mu tona domin ta yaya zamu tattauna batun gyaran tattalin arzikin kasar mu ba tare da yin waiwayen baya ba domin ganin inda aka samu matsala da kuma kiyaye afkuwar irin hakan a gaba?," a cewar Osinbajo.

DUBA WANNAN: An yi dauki ba dadi tsakanin ma su sayarwa da shan kwayoyi a Jos, hankuka sun tashi

Osinbajo ya jajanta yadda gwamnatin baya ta Jonathan ta gaza ajiye komai a asusun Najeriya duk da irin kudin da gwamnatin ta samu a lokacin da man fetur keda daraja a duniya.

Kazalika, mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewar babu abinda zai hana tattalin arzikin Najeriya samun matsala da irin wadannan hujoji da kudaden da ya kamata a yi aiyuka da su ko su shiga asusun gwamnati ke zurarewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng