An yi dauki ba dadi tsakanin ma su sayarwa da shan kwayoyi a Jos, hankuka sun tashi
An samu barkewar rikici tsakanin ma su sha da sayar da miyagun kwayoyi a yankin Congo-Russia, daya daga wuraren da su ka yi kaurin suna ta fannin aikata laifuka.
Wani shaidar gani da ido ya ce kadan ya rage rikicin 'yan kwayar ya rikide zuwa na addini. Shaidar ya ce rikicin ya samo asali ne bayan samun labarin jita-jitar cewar an tsinci gawar wasu Hausawa biyu da aka kashe a unguwar Gada Biyu a cikin wani ruwa.
Shaidar, Ibrahim Audu, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar, 'yan kwayar sun kusan mayar da rikicin na addini ba don Allah ya sa jagororin al'umma da jami'an kwantar da tarzoma sun gaggauta shiga tsakani ba.
DUBA WANNAN: Muna iyakar kokarinmu amma babu ranar kubutar da ‘yan matan Dapchi – Ministan tsaro
"Bamu ankara sai ganin daruruwan matasa mu ka yi dauke da sanduna da makamai su na ihu "an fara", amma sai jagororin al'umma su ka tsaya kai da fata don ganin ba a samu barkewar rikicin ba ta hanyar tsawatar wa matasan kafin karasowar jami'an tsaro," a cewar Adamu.
Manjo Adamu Umar, jami'in hulda da jama'a na OPSH ya ce, batun kisan mutane biyu a Gada-Biyu ba gaskiya bane tare da bayyana cewar takaddama ce tsakanin 'yan kwayar a kan samamen da hukumar NDLEA ta kawo ya fara haddasa matsalar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng