Shugaban Majalisan Dattawa Bukola Saraki yayi ta'aziyya ma Gwamnatin Bauchi Sarkin Bauchi da iyalin Ali Wakili
- Dakta Bukola Saraki yayi wa gwamnatin da al’ummar jihar Bauchi ta’aziyar rasauwar Sanata Ali Wakili
- Saraki ya ce mutuwar Sanata Ali Wakili babban rashin ne ga Najeriya
Wata babban tawaga da daga majalissar dattawan Najeriya karkashin jagorancin, Sanata Bukola, sun kai ziyarar ta’aziya ma Gwamnatin Bauchi Sarkin Bauchi da iyalin marigayi Ali Wakili akan mutuwar abokin su.
Allah yayi wa Sanata Ali Wakili rasuwa ne a ranar Asabar da gabata a birnin Abuja bayan ya yanke jiki ya fadi bayan kirjin sa ya buga.
Wannan tawaga ta kai ziyara fadar Mai martaba Sarkin Bauchi, Eng Alh Dr Rilwanu Sulieman Adamu CFR, a safiyar yau litinin 19 ga watan Maris 2018.
KU KARANTA : Hukumar DSS ta bayana yadda ta kama wani shahararren mai safarar makamai a Najeriya
Shugaban majalissar dattawa Dakta Bukola Saraki, yace mutuwar Sanata Ali wakili ba rashi bane kadai ga jihar Bauchi babban rashi ne ga kasar baki daya, saboda irin gudumawar dan majalisar ya bayar wurin cigaban kasar.
A karshen Sanatocin sunyi wa marigayi, Sanata Ali Wakili, adu’oi, Allah ya gafarta masa dukan zunnuban sa kuma Allah yayi masa Rahama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng