Yau take daya ga watan Rajab, inji Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III
Shugaban kwamitin shura na addinin musulunci a Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ya bayyana yau, Litinin; 19 ga watan Maris, a matsayin ranar farko ta watan Rajab, hijira ta 1439AH.
Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda da shugaban kwamitin harkokin addinin Islama kuma wazirin sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali, ya sanyawa hannu, tare da bayyana cewar sun fitar da sanarwar ne sabida da rashin samun rahotonton ganin sabon wata.
"Kwamitin tuntuba a kan harkokin addini tare da hadin gwuiwar kwamitin duban wata na su samu rahoton ganin sabon wata ba daga sassan kasar nan a ranar Asabar 17 ga watan Maris, da tayi daidai da 29 ga watan Jimada 1439AH.
DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Jarrabawar gwajin malaman makarantun sakandire na nan tafe - El-Rufa'i
"Mai martaba sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin Islama, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya amince da rahoton rashin ganin watan, tare da bayyana ranar litinin, 19 ga watan Maris, a matsayin ranar farko a watan Rajab 1439AH."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng