Najeriya zata iya samar da wutan lanatarki mai karfin megawatt 7,000 - Fashola
- Babatunde Fashola ya ce Najeriya zata iya samarwa da raba wutan lantarki maikarfin megawatt 7,000
- Fashola ya ce kokarin da suka yi a fannin wutan lantarki yasa mutane sun rage amfani da na'urar Janareta a Najeriya
Ministan wutan lantarki da gidaje, Mista Babatunde Fashola, yace yanzu kasar zata iya samar da wutar lantarki mai karfin Megawat 7,000.
Fashola ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a taron manema labaru da aka gudanar birnin Abuja, inda ya ce sun samar da hanyoyin raba wutar lantarki da suke yunkurin samarwa.
Ministan ya ce, ba samar da wutar lantarki ma yawa bane matsalar su, matsalar su shine raba wutan lantarkin.
KU KARANTA : Yaki da cin hanci da rashawa: Tsohon mataimakin shugaban kasa ya sha tsumagiya, bulala 80 da dauri
“Shekaru biyu da suka gabata ne kamfanonin raba wutar lantarki suke ta korafin cewa basu da isashen wutan lantarki da a sa sayar kwastomomin su, amma yanzu labari ya canza.
"Yadda mutane ke amfani da janareto saboda rashin wutan lanatarki a da yayi matukar raguwa a yanzu saboda irin cigaba da aka samu a fannin wutan lantarkin kasar,”Inji Fashola.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng